• Iraki: Isis ta kashe Fararen Hula 30 A Garin Al Huwaijah.

Tashar Telbijin din Somariyyah ta kasar Iraki ta ce; Mafi yawancin mutanen da Da'esh din ta kashe a garin na Huwaijah da ke gundumar Karkuk, mata ne da kananan yara.

Tashar Telbijin din Somariyyah ta kasar Iraki ta ce; Mafi yawancin mutanen da Da'esh din ta kashe a garin na Huwaijah da ke gundumar Karkuk, mata ne da kananan yara.

Anwar al-Asy, wanda daya ne daga cikin jagororin kabilar al Ubaid, ya cce;Daga 2014 zuwa yanzu,kungiyar 'yan ta'addar ta Da'esh ta kashe mutanen da su ka kai 1000.

A gefe daya, sojojin kasar ta Iraki da su ke fada da kungiyar Da'esh, sun kutsa cikin unguwanni na karshe da su ka saura a hannun kungiyar ta 'yan ta'adda a cikin birnin Musel. Kawo ya zuwa yanzu dai an kashe da dama daga cikinsu da kuma kame wasu.

Jun 19, 2017 10:56 UTC
Ra'ayi