• Peter Ford: Iran Ta Aike Da Babban Sako Da Makamai Masu Linzami

Tsohon jakadan Birtaniya akasar Syria Peter Ford ya bayyana cewa, Iran ta aike da babban sako mai girgiza zukata ta hanyar harba makaman ballistic zuwa sansanonin 'yan ta'adda a cikin kasar Syria.

Peter Ford ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da tashar RT a yau, inda ya ce sakon da Iran ta aike da shi ya wuce batun 'yan ta'adan ISIS, sako ne ga iyayen gidan ISIS, Amurka da Saudiyya.

Ya ci gaba da cewa  babu wanda ya yi zaton cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi irin wannan sakamakon harin da 'yan ISIS suka kai birnin Tehran a cikin 'yan kwanakin da suka gabata.

To amma kuma hakan da ta yi ya sanya ala tilas duk masu hannu cikin shirya harin da aka kai a Tehran su gyara zama, ya ce ga alama Iran ta tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro.

Jun 19, 2017 17:33 UTC
Ra'ayi