• Saudiyya : Ba Sassauci A Sharuddan Da Muka Gindayawa Qatar

Saudiyya da kawayenta na kasashen Larabawa da suka hadu yau a birnin Alkahir ana Masar sun ce babu wani sassauci a sharuddan da suka gindayawa kasar Qatar kafin su maido da huldarsu da ita.

Haduwar ta tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen da suka hada da Masar, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain sun hadu ne a Masar domin nazari akan mataki na gaba da zasu dauka kan kasar ta Qatar.

A ranar biyar ga watan Jiya ne kasashen suka katse duk wata irin  hulda da kasar ta Qatar bisa zarginta da taimakawa ayyukan ta'addanci da kuma dasawa da kasar Iran.

domin kawo karshen wannan takaddama kasashen sun gindawa Qatar sharudu 13 da suka hada da rufe wani sansanin sojin Turkiyya a Qatar din, da rufe gidan talabijin na Al'Jazeera da kasar ke gudanarwa da kuma rage alakarta da kasar Iran.

A ranar Litini data gabata dai Kasar Qatar ta yi fatali da dukkan shaduddan wadandan ta danganta da cin fuska da kuma keta hurimin kasar.

A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen kasar ta Qatar ya bayyana a wani taro a birnin Landan cewa, kasarsa a shirye take don zama teburin tattaunawa aman da sharaddin mutunta hurumin kasar.

Tags

Jul 05, 2017 14:34 UTC
Ra'ayi