• Syria: Fiye Da 'Yan Gudun Hijira 600,000 Ne Su ka Koma  Kasarsu

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da komawar fiye da 'yan kasar Syria 600,000 da su ke rayuwa a kasashen waje.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato kakakin hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Olivia Headon tana cewa; Daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekarar 'yan gudunhijira 602,000 da 759 ne su ka koma kasarsu, kuma ana hasashen cewa za su karu.

Olivia Headon ta kara da cewa; kaso 90 % na wadanda su ka zama 'yan gudun hijira a cikin gida, sun koma gidajensu.

'Yan gudun hijirar da su ka koma kasar tasu, sun fito ne daga kasashen Turkiya, Lebanon, Jordan da Iraki.

Shekaru 6 kenan ajere kasar Syria tana fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da su ka hada al'ka'ida da Da'esh.

 

Aug 12, 2017 09:19 UTC
Ra'ayi