• Rikici Tsakanin 'Yan Ta'adda A Kasar Siriya Ya Lashe Rayukan Mutane Masu Yawa

Harin kunan bakin wake da aka kai sansanin 'yan ta'addan Jaishul-Islam da ke cikin kasar Siriya kusa da kan iyaka da kasar Jordan ya lashe rayukan mutane akalla 23 tare da jikkatan wasu 12 na daban.

Tashar Sky news a safiyar yau Asabar ta watsa rahoton cewa: Wani dan kunan bakin wake da ya makare motarsa da bama-bamai ya tarwatsa kansa a sansanin 'yan ta'addan kungiyar Jaishul-Islam da ke kusa da kauyen Nasib na kasar Siriya kusa da kan iyaka da kasar Jordan, inda harin ya lashe rayukan 'yan ta'adda akalla 23 tare da jikkata wasu 12 na daban.

Har ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko jama'ar da ta dauki alhakin kai harin, amma harin baya rasa nasaba da irin sabanin da ke tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda da suke yaki a kasar ta Siriya.    

Aug 12, 2017 12:03 UTC
Ra'ayi