• Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kai Hari A Wani Masallaci A Yankin Aizariyyah

Jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmakia kan masallaci Abu Hurairah a dake yankin Aizariya gabashin birnin Quds.

Tashar arab48 ta bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron yahudawan sun kaddamar da farmaki a jiya, inda suka kutsa kai cikin masallacin tare da cin zarafin musulmin da suke gudanar da salla a cikin masallacin, tare da yin awon gaba da wasu daga cikin su.

Yasuf Adis shi ne minister mai kula da harkokin addini a gwamnatin kwarkwaryan cin gishin kai ta Palastinawa, ya bayyana wannan aiki da cewa ya munana matuka, musamman ma ganin cewa masallaci jami’an tsaron Isra’ila suka keta alfarmartsa a lokacin da musulmi suke yin salla.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin wuraren musulmi da suka hada da masallatai da sauran cibiyoyinsu da kuma wuraren tarihinsu mallakin musulmi ne, yahudawa ba su da hakkin shiga wadannan wurare, kumayin hakan yana a mtsayin tsokana.

Daga karshe ya kirayi kasashen musulmi da ma sauran kasashe masu sauran lamiri da su dafa wa al’ummar Palastinu domin kawo karshen zalunci da kuma danniyar Isra’ila a kansu.

Aug 13, 2017 05:27 UTC
Ra'ayi