• Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Sun Kashe Mutane 12 A Garin Karkuk Na Kasar Iraki

Yan ta'addan kungiyar Da'ish sun aiwatar da kisan gilla kan wasu Irakawa fararen hula 12 a yankin Alhuwaijah da shiyar kudu maso yammacin garin Karkuk na kasar Iraki.

Shafin watsa labaran Sumariyyah News ya bayyana cewa: 'Yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish sun kame mutane ne suna kokarin tserewa daga yankin na Alhuwaijah da ke karkashin ikon 'yan ta'adda, inda suka zo da su bainar jama'a suka kashe su a jiya Alhamis.

Kamar yadda kungiyar ta'addancin ta Da'ish ta sanar da cewar zata kashe dukkanin jama'ar da ta kama kuma take tsare da su a gidan kurkukun yankin na Alhuwaijah da ke garin Karkuk.

A nata bangaren gwamnatin Iraki a ta bakin kwamandan rundunar sojin kasar ta sanar da shirinta na hanzarta kai dauki ga al'ummar yankin na Alhuwaijah da nufin yantar da su daga kangin zaluncin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish.

Sep 08, 2017 06:37 UTC
Ra'ayi