• Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Da Japan Sun Jaddada Bukatar Kafa Kasar Palasdinu

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na Japan sun jaddada goyon bayansu ga shirin samar da kasar Palasdinu mai cikekkiyar gashin kai da Qudus zai kasance babban birninta.

A bayan kawo karshen zaman taron hadin gwiwa kan harkokin siyasa tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da kasar Japan a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Litinin: Mahalatta zaman taron sun fitar da bayani da ya kunshi goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da jaddada bukatar kawo karshen gine-ginen matsugunan Yahudawa Sahayoniyya 'yan kaka gida a yankunan Palasdinawa kamar yadda kudurin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada hakan.

Har ila yau mahalatta zaman taron na birnin Alkahira sun yi tofin Allah tsine kan killace yankin Zirin Gaza tare da hanzatar kawo karshen wannan bakin zalunci.    

Sep 12, 2017 11:44 UTC
Ra'ayi