• Wasu Kasashen Larabawa Sun Yanke Taimakon Kudin Da Suke Baiwa Gwamnatin Palastinu

Wasu daga cikin kasashen Larabawa su kudiri yanke taimakon kudaden da suke bawa gwamnatin Palastinu daga watan oktoba mai kamawa.

Kafar watsa labaran Palastinu ta nakalto manyan jami'an gwamnatin Palastinu na cewa alakar dake tsakanin gwamnatin Palastinu da wasu kasashen larabawa musamman ma kasashen yankin tekun Fasha ta fada cikin wani yanayi, lamarin da ya sanya wasu daga cikin su suka kudiri aniyar yanke taimakon kudin da suke bawa gwamnatin ta Palastinu.

Rahoton ya ce wannan mataki da wasu kasashen larabawan suka dauka zai iya jefa gwamnatin ta Palastinu cikin mawuyacin hali ta yadda ba za ta iya biyan ma'aikatanta albashi a lokaci ba.

Kasashen da suka hada da Masar, Qatar da Oman, saboda matsalar tattalin arziki da suke fuskanta da kuma faduwar farashin man fetir a duniya gami da  rikicin dake tsakanin kasashen Larabawa na yankin tekun fasha, sun ce ba za su iya ci gaba da bawa gwamnatin Palastinu taimakon kudaden da suke bata na shekara-shekara ba.

Sep 13, 2017 05:52 UTC
Ra'ayi