• Fira Ministan Iraki Ya Ce Shirin Ballewar Yankin Kurdawa Daga Kasar Ya Saba Doka

Fira ministan Iraki ya jaddada cewa: Shirin gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a da mahukuntan yankin Kurdawar kasar ke yi dangane da neman ballewa daga kasar ta Iraki ya sabawa doka.

Fira ministan Iraki Haidar Abadi a yau Laraba ya jaddada cewa: Shirin mahukuntan yankin Kurdawar kasar na gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan makomar yankin lamari ne da ya sabawa doka, don haka yake jaddada yin kira ga mahukuntan yankin na Kurdawa kan gudanar da zaman tattaunawa da gwamnatin Iraki.

Tun a ranar 7 ga watan Yunin wannan shekara ce wasu jam'iyyun siyasa da kungiyoyin yankin Kurdawa mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Iraki karkashin jagorancin shugaban yankin Mas'ud Barazani suka yanke shawarar gudanar da zaben jin ra'ayin jama'ar yankin kan batun neman ballewa daga kasar Iraki da nufin kafa kasarsu ta Kurdawa, inda suka tsayar da ranar 25 ga watan Satumban wannan shekara ta 2017 a matsayin ranar gudanar da zaben. 

Sep 13, 2017 12:20 UTC
Ra'ayi