• Yemen: An Yi Tattaunawa A Tsakanin Tsohon Shugaban Kasa Abdallah Saleh Da Jagoran 'Yan Huthi.

Tattaunawar a tsakanin Abdulmalik Badruddin al-huthy da Ali Abdullah Saleh ta maida hankali ne akan dinke barakar da ke tsakaninsu domin kalubalantar makiya.

Tashar telbijin din al-masirah ta kungiyar Ansarullah ta bada labarin cewa; Tattaunawar da aka yi a yau laraba ta tabo muhimman abubuwan da suke faruwa a kasar ta Yemen da kuma alakar da take a tsakanin kungiyar Ansarullah da kuma jam'iyyar "Mu'utumar al-sha'abi," ta Ali Abdallah Saleh."

Har ila yau bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ci gaba da kare hadin kan al'ummar kasar domin fada da 'yan mamaya da hana su cimma burinsu.

Saudiyya da kawayenta ta fara kai wa kasar Yemen hari tun a 2015 bisa jagorancin Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka fiye da 12,000.

Sep 13, 2017 18:59 UTC
Ra'ayi