Sep 14, 2017 16:32 UTC
  • Iraki : An Tsige Gwamnan Kirkuk

Majalisar tarayya a Iraki ta amunce da gagarimin rinjaye da tsige gwamnan yankin Kirkuk, Najm Eddine Karim saboda nuna goyan bayansa ga kiran zaben raba gardama na kafa kasar Kurdawa.

'Yan majalisa 173 ne suka amunce da tsige gwamnan bisa bukatar firayi ministan kasar Haider al-Abadi, duk da cewa 'yan majalisar dake wakiltar yankin na Kurdawa basu halarci zaman ba.

Saidai gwamna na Kirkuk ya ce ya kalubalanci tsigewar da aka masa yana mai cewa majalisar yankinsa ce ta bashi yarda don haka babu wani mahaluki da ya iasa ya tsige shi, ba wai firayi minista ba ko kuma majalisar ta Iraki.

A karshen watan Agustan da yagaba ne majalsar shawara ta yankin na Kirkuk ta amunce da shirin gudanar da zaben raba gardama a yankin a ranar 25 ga watan Satumban nan duk da kin amuncewar gwamnatin Bagadaza, batun da ya tayar da kace nace ba kadan ba a yankin.

kawo yanzu H.k Isra'ila ce kawai ta fito filoi tana mai goyan bayan ballewar Luirdawa domin kafa kasarsu ta kansu, a yayin da Amurka ta bukaci a dan jinkirta batun saboda zai iya kawo cikas a hadakar da ake da Kurdawan kan yaki da 'yan ta'adda na Da'esh a Iraki.

Ita kuwa Turkiyya ta yi gargadi ne ga Kurdawan akan abunda zai iya biyo bayan ballewarsu.

Tags

Ra'ayi