Sep 21, 2017 04:05 UTC

A ranar Talatar da ta gabata ce sakataren tsaron kasar Birtaniya Michael Fallon ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Saudiyya, inda ya gana da Muhammad bin Salman yarima mai jiran gado a garin Jiddah, kuma jami'an kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu.

Har ila yau a ganawar da ta gudana tsakanin Michael Fallon sakataren tsaron kasar Birtaniya da Muhammad bin Salman yarima mai jiran gado na Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sayar da makamai da taimakekkeniyar tsaro da na soji a tsakanin kasashensu gami da tattauna batun matsalolin tsaro da suke ci gaba da adabar yankin gabas ta tsakiya dama duniya baki daya.

A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan jami'an gwamnatin Birtaniya ciki har da fira ministan kasar Theresa Mary May sun yawaita gudanar da ziyarar aiki zuwa kasashen Larabawan yankin tekun Pasha ciki har da kasar Saudiyya, kuma ziyarar aikin ta fi maida da hankali ne kan kulla cinikin makamai da samun damar ci gaba da jibge sojojin kasar ta Birtaniya a cikin kasashen yankin.

Tun a watan Nuwamban shekara ta 2016 kasar Birtaniya ta samu damar kafa sansanin sojinta a kasar Bahran, sannan jami'an kasar ta Birtaniya suka ci gaba da gudanar da jigila zuwa kasashen Kuwait, Qatar, Saudiyya da Oman da nufin bunkasa alaka da taimakekkeniya a tsakaninsu musamman a fagen sayar da da makamai, kuma kasancewar Saudiyya a matsayin kasa mafi muhimmanci da arziki a tsakanin kasashen Larabawan yankin taken Pasha, sakamakon haka mahukuntan Birtaniya suka fi maida hankali kan kulla yarjejeniyar tsaro da na makamai da ita.

Kasar Birtaniya kamar sauran kasashen yammacin Turai, sun rufe idonsu kan yadda kasar Saudiyya take ci gaba da take hakkokin bil-Adama a ciki da wajen kasarta musamman yadda take kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen tana kashe mata da kananan yara gami da tsofaffi, inda tun a shekara ta 2015 yarjejeniyar makamai da ke tsakanin kasar Saudiyya da Birtaniya ta kai na tsaban kudi kimanin dalar Amurka biliyan hudu. 

A gefe guda kuma duk da tarin rahotonni da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suke fitarwa dangane da kashe-kashen gillar da masarautar Saudiyya take yi a kasar Yamen tare da rusa duk wani abu mai amfani a kasar ta hanyar amfani da muggan makamai amma gwamnatin Birtaniya ta yi kunnen uwar shegu tana ci gaba da kulla yarjejeniyar sayar da makamai ga mahukuntan kasar ta Saudiyya, kuma ziyarar aikin da sakataren tsaron Birtaniya Micheal Fallon ya kai zuwa kasar ta Saudiyya a cikin 'yan kwanakin nan, tana daga cikin bakar siyasar Birtaniya ta taimakawa mahukuntan Saudiyya a fagen ci gaba da aiwatar da bakar siyasarta ta zalunci.      

Tags

Ra'ayi