• Siriya : IS Ta Dauki Alhakin Kai Jerin Hare-haren Damascos

Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta ce ita keda alhakin kai jerin hare-haren kunar bakin waken da aka kai a barikin 'yan sanda Birnin Damascos.

A sanarwar data fitar kungiyar ta ce mambobinta ne suka kai jerin hare-haren uku da suka yi sanadin mutuwar mutane uku a yau Laraba.

Kafin hakan dai wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar Siriya ta fitar ta nuna cewa 'yan sanda biyu ne suka gamu da ajalinsu a jerin hare haren sai kuma wasu mutum shida da suka raunana ciki har da yara biyu.

Saidai a wani rahoto data fitar kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa a Siriya OSDH ta ce mutane biyar ne suka rasa rayukansu a jerin hare haren uku.

Wannan dai shi ne karo na biyu a kasa da makwanni biyu da ake kai ire iren wadannan hare hare a Damascos babban birnin kasar ta Siriya wanda kuma kungiyar 'yan ta'addan ta IS ke daukar alhakin kaiwa.

Tags

Oct 11, 2017 18:18 UTC
Ra'ayi