• Sojojin Syria Sun Rusa Wuraren Harba Makamai Masu Linzami Na 'Yan Ta'adda A Halab.

Tashar telbijin din al'alam ta bada labarin cewa a jiya laraba ne sojojin na Syria sun kai harin ne a yankunan Lirmon da Rashidin da ke kusa da Halab.

Harin ya yi sanadin rusa wuraren da 'yan ta'addar ke amfani da su wajen harba makamai masu linzami da rokoki.

A gefe daya, wata mota mai makare da abubuwan fashewa ta tarwatse tare da wasu 'yan kungiyar jubhatun Nusrah, ta 'yan ta'adda su 4, inda suka halaka nan take.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai wannan harin.Sai dai a ranar litinin din da ta gabata an yi fada mai tsanani a tsakanin kungiyar ta Nusrah da kuma "Ahrarus-sham' a garin Armanaz, da ya kare da samun galabar Nusrah, ta hanyar shimfida ikonta a yammacin Adlib.

 

Tags

Oct 12, 2017 06:24 UTC
Ra'ayi