Oct 28, 2017 06:29 UTC
  • Iraki Ta Dakatar Da Aikin Soji Na Sa'o'i 24 A Yankunan Da Ake Takaddama

Firayi ministan Iraki, Haïder al-Abadi, ya bada umurnin dakatar da duk wani aikin sojin kasar na sa'o'i 24 a yankunan da ake takaddama akansu.

Sanarwar da aka fitar ta ce Al-Abadi ya baiwa sojojin kasar umurnin su dakatar da duk wani aiki na tsawan sa'o'i 24 a arewacin kasar da kuma yankunan da gwamnatin Erbil take cewa nata ne.

Manufar hakan a cewar sanarwar shi ne samun lokaci na jibge dakarun gwamnatin kasar a wuraren da ake takaddama akansu.

Kafin hakan dai kwamitin sulhun na MDD ya bayyana damuwa matuka game da yadda ake samun rahotannin karuwar zaman tankiya tsakanin sojojin gwamnatin Iraki da mayakan Kurdawa.

Jakadan kasar Faransa a MDD, Francois Delattre ya bayyana a yayin zaman kwamitin cewa daukacin mambobin kwamitin sun bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su koma kan teburin sulhu a matsayin hanya mafi dacewa ta hana barkewar duk wani tashin hankali a kasar, maimakon amfani da karfi ko barazana.

A cewar mambobin, muddin ana bukatar a kare 'yanci da hadin kan kasar Iraki, to wajibi ne a dauki matakan da suka dace na yakar kungiyar IS.

 

Tags

Ra'ayi