Oct 30, 2017 11:46 UTC
  • Kungiyar Arab League Ta Yi Tofin Allah Kan Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kasar Somaliya

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a ranar Asabar da ta gabata.

A bayanin da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Ahmad Abul-Gheit ya fitar yana dauke da tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai kan wani otel a tsakiyar birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a ranar Asabar da ta gabata, inda harin ya lashe rayukan mutane akalla 30 tare da jikkata wasu adadi masu yawa da aka kiyasta cewa sun haura 50.

Abul-Gheit ya jajanta wa iyalan mutanen da harin ya ritsa da 'yan uwansu tare da jaddada matsayin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa na ci gaba da goyon bayan gwamnatin Somaliya a yakin da take yi da ta'addanci.

Tags

Ra'ayi