Nov 27, 2017 06:34 UTC
  • Yemen : Tallafin Farko Ya Shiga Yankin Da 'Yan Houthi Ke Rike Da

MDD, ta sanar da cewa wani jirgin ruwa dauke da tallafin abinci ya samu isa tashar ruwa ta yammacin kasar Yemen, wanda shi ne na farko cikin makwanni uku a yankin da 'yan gwagwarmaya na Houthi ke rike da.

Kakakin hukumar abinci ta MDD (WFP), mai kula da yankin gabas ta tsakiya da kudancin AFrika, Abir Atifa, ya bayyana cewa ton 25,000 ne na alkama za'a saukewa yau Litini, kasancewar hakan bata samu ba a jiya saboda rashin kyawon yanayi.

Tashar ruwa ta Salif dake kusa da yankin Hodeida, nan ne al'umma Yemen ke cikin matsanancin bukatar tallafi.

A ranar 6 ga watan Nuwamban nan ne, kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya rufe duk iyakokin sama dana ruwa da kasa bayan harba wani makami mai linzami da 'yan Houthi suka yi zuwa birnin Riyad, domin maida martani akan hare-hare zalincin shekaru biyu da Saudiyyar ke kai masu ba kakkautawa.

Saudiyya dai ta amunce bude hanyoyin ne bayan shan matsin lamba daga MDD, wadda ta bukaci hakan saboda halin da al'ummar ta Yemen zasu iya kara fadawa.

Tags

Ra'ayi