• Yemen: An Kai Wa 'Yan Koren Saudiyya Hari A Saharar Meden.

Mayakan Ansarullah sun harba makamai masu linzami samfurin Zilzal 1 akan 'yan koren Saudiyya a saharar Meden da ke gundumar Hajjah.

Tashar telbijin din al-alam, ta ambato majiyar tsaron kasar Yemen na cewa; bayan harba makaman masu linzami samfurin zilzal1 guda biyar, ,mayakan Ansarullah sun kuma harba manyan bindigogi.

A gefe daya Saudiyya ta sanar da cewa mayakanta 4 sun halaka sanadiyyar harin da aka kai musu akan iyaka daga kasar Yemen.

Bugu da kari  jiragen yakin Saudiyya sun kai wasu hare-haren a cikin kasar Yemen da suka hada da babban birnin kasar Sanaa.

Tun a cikin watan Maris na 2015 ne dai Saudiyya da kawayenta suka fara kai wa kasar Yemen hari, wanda kawo ya zuwa ta kashe fararen hula fiye da 12,000.

Dec 06, 2017 06:26 UTC
Ra'ayi