• An Cimma Yarjejeniyar Tsakanin Gwamnati Da 'Ya'yan Gidan Sarautar Saudiyya Da Suke Tsare

Ma'aikatar shari'ar kasar Saudiyya ta sanar da cewa da dama daga cikin 'ya'yan gidan sarautar kasar da sauran masu kudin da ake tsare da su bisa zargin rashawa da cin hanci sun amince da wata yarjejeniya ta kudi da aka cimma da su kafin a sako su daga inda ake tsare da su.

Kafafen watsa labaran Saudiyya sun jiyo Antoni janar na kasar Sheikh Saud al-Mojeb yana fadin cewa mafi yawa daga cikin mutane 159 da ake tsare da su sun amince da wata yarjejeniya da aka kulla da su na su dawo da wasu makudan kudi cikin asusun gwamnati don a sake su.

Kafin hakan dai Sheikh al-Mojeb ya ce mutanen da ake tsare da su din sun yi watandar kudaden da suka kai Dala biliyan 100 daga asusun gwamnatin tsawon shekaru ta hanyoyi daban-daban don haka ne aka tsare su da nufin dawo da wadannan kudaden asusun gwamnatin.

A kwanakin baya ne dai yarima mai jiran gado na Saudiyyan Muhammad bn Salman ya ba da urmurnin kama wadannan 'ya'yan gidan sarautar da kuma wasu hamshakan masu kudi a kasar bisa zargin rashawa da cin hanci lamarin da da dama suke ganin akwai batun siyasa cikin lamarin a kokarin da Yariman yake yi na rufe bakin duk wani da zai yi adawa da shirinsa na darewa karagar mulkin kasar.

 

Tags

Dec 06, 2017 11:14 UTC
Ra'ayi