• Kwamitin Tsaron MDD Ya Bayyana Tsananin Damuwarsa Kan Matsalar Kasar Yamen

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwarsa kan halin tsaka mai wuya da al'ummar kasar Yamen suke ciki, tare da jaddada bukatar dakatar da bude wuta domin aikewa da kayayyakin jin kan bil-Adama cikin kasar.

A ganawarsa da manema labarai a jiya Talata bayan kammala zaman kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan matsalar yankin gabas ta tsakiya musamman matsalar kasar Yamen: Shugaban kwamitin tsaron na karba-karba Jakadan kasar Japan Koro Bessho ya bukaci dukkanin bangarorin da suke fada da juna a kasar da su dauki matakin dakatar da bude wuta ba tare da gindaya wani sharadi ba saboda Majalisar Dinkin Duniya ta samu damar aikewa da kayayyakin jin kan bil-Adama cikin kasar.

Koro Bessho ya kara da cewa: A rahoton da suka samu akwai mutane kimanin miliyan takwas da suke fama da matsalar karancin abinci a Yamen sakamakon bullar matsalar fari da kuma hare-haren wuce gona da iri kan kasar.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ne masarautar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yamen da nufin dawo da tsohon shugaban kasar mai ritaya Abdu-Rabbuh Mansur Hadi kan karagar shugabancin kasar domin samun damar ci gaba da aiwatar da bakar siyasarta ta zalunci kan al'ummar Yamen.  

Tags

Dec 06, 2017 18:56 UTC
Ra'ayi