• Martanin Jaridun Kasashen Turai Kan Matakin Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka A Kan Quds

Jaridun kasashen Turai sun yi suka kan matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka na amincewa da birnin Quds a matsayin cibiyar gwamnatin HKI.

Jaridar Guardian ta kasar Britaniya ta rubuta cikin shafuffukanta a yau Alhamis kan cewa matakin da shugaba Trump ya dauka zai haifar da mummunan sakamako ga Amurkan da kuma kasashen Larabawa.

Jaridan ta kara da cewa dauke ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds zai gamu da maida martani wanda a halin yanzu ba zamu iya sawwarashi ba. 

Sai kuma jaridar Le monde ta kasar Faransa wacce ta rubuta cewa dukkan shuwagabannin kasashen Larabawa da na kasashen Turai sun yi Allah wadai da matakin da shugaba Donal Trump ya dauka na maida birnin Quds ya zama cibiyar gwamnatin HKI. 

Sai kuma jaridar "Liberation" ita ma ta kasar Faransa tana cewa dangane da wannan batun Daga Paris zuwa Tehran, daga Vatican zuwa Istambul, daga Brussels zuwa Alkahira dukkan shuwagabannin wadan nan kasashe sun ja kunnen Trump kan wannan matakin amma bai sauraresu ba.

Tags

Dec 07, 2017 11:46 UTC
Ra'ayi