Dec 10, 2017 11:51 UTC
  • Kasar Algeria Ta Ki Amincewa Amurka Shigo Da Sojojinta Kasar Don Kare Ofishin Jakadancinta A Kasar

Gwamnatin kasar Algeria ta yi watsi da bukatar ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka na shigo da sojojinta cikin kasar don kare ofishin jakadancinta a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar diblomasiyar kasar Algeria tana cewa gwamnatin kasar ba zata amincewa Amurka mta shigo da sojojinta (Merin) cikin kasar don kare ofishin jakadancin kasar ta dake cikin birnin Algies ba. 

Majiyar ta kara da cewa jami'an tsaro na musamman wanda gwamnatin kasar ta ware don kare ofisoshin jakadancin kasashen waje a kasar ne zasu yi wannan aikin.

A ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurka ta bukaci gwamnatocin kasashen Larabawa da musulmi da su amince mata ta shigo da sojojin ta kasashensu don kare ofisoshin jakadancinta da ke kasashen. Ma'aikatar ta dauki wannan matakin ne bayan da shugaban kasar Donald Trump ya bada sanarwan amince da birnin Qudus ya zama cibiyar gwamnatin HKI a ranar Laraba.

Yanzu haka wasu rahotanni da suke fitowa daga kasar Lebanon na nuni da cewa, ana bata kashi tsakanin masu zanga-zanga da kuma jami'an tsaro a gaban ofishin jakadancin Amurka  abirnin Beirut, da suke yin kira da a rufe ofishin jakadancin Amurka a kasarsu, sakamakon kudirin na Trump dangane da birnin Quds.

Tags

Ra'ayi