• An Dage Haramcin Zuwa Kallon Sinima A Saudiyya

Mahukuntan Saudiyya sun sanar da dage haramcin tsawan fiye da shekara talatin da suka wuce kan zuwa gidajen kallon sinima a fadin kasar.

Gwamnatin kasar dai ta ce za ta fara bada lasisi domin ganin gidajen na kallon sinima sun bude kofofinsu a watan Maris na shekara 2018 dake tafe.

Shirin dai ya tanadi bude gidajen kallon sinima sama da 300 da kuma mayen akwatinan talabijin sama da 2,000 kafin nan da shekara 2030 a cewar ma'aikatar al'adu da yada al'adu ta kasar ta sanar.

Wannan matakin dai na daga cikin gagarimin shirin nan mai taken ''Vision 2030'' na yarima mai jiran gado, Mohamed Ben Salman, na ganin an rage dogoro kacokam da man fetur a wannan kasa mai tsatsauran ra'ayin addini na wahabiyanci.

A watan Afrilu na shekara 2016 data gabata ne matashin yariman dan shekaru 32 ya gabatar da shirin mai taken ''hangen 2030'' wanda tuni masu sharhi kan lamuran yau da kulun suka danganta da yunkurin yariman na kakkabe kasar daga tsatsauran ra'ayin addinin Islama.

Shirin dai na Ben Salman ya shan suka daga mayan maluman addini na kasar masu ra'ayin rikau.

Tags

Dec 11, 2017 14:38 UTC
Ra'ayi