Dec 11, 2017 16:08 UTC
  • Qudus : Matakin Trump, Ayyana Karshen Isra'ila Ne _ Nasrallah

Shugaban Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa matakin Trump na Amurka kan ayyana Qudus babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya shelanta kawo karshen Isra'ila ne.

Sayyid Nasrollah na bayyana hakan ne a yayin wani jawabinsa, bayan zanga zangar da kungiyar ta Hezbollah ta kira a yau Litini don la'antar matakin shugaban Amurka na mallakawa yahudawan sahayoniya birnin Qudus.

Haka zalika kuma shugaban kungiyar ta Hezbollah, ya ce bayan murkushe kungiyar 'yan ta'adda musamen a Siriya, yanzu lokaci ne na sadaukar da kai ga Palastinu.

Irin wannan sadaukarwa a cewar Sayyid Nasrollah ita ce ya kamata kasashen Larabawa su yi ga al'ummar Palastinu, domin mu kasance milyoyin shahidai akan ''Jérusalem''

Dubun dubatar al'ummar Labanon ne suka shiga zanga zangar suna masu rera taken '' mutuwa ga Amurka da Isra'ila'' 

Masu zanga zangar da ke dauke kuma da tutar Palastinu data kungiyar Hezbollah suna kuma dauke da alluna dake dauke da rubutun cewa '' Palastinu tamu tamu ce''.

Koa jiya ma dubban al'ummar Labanon sun gudanar da zanga-zanga a kusa da ofishin jakasancin Amurka dake arewacin birnin Beirut.

 

Tags

Ra'ayi