• Hamshakin Mai Kudin Nan Na Saudiya Talal Bn Abdul-Azez Ya Shiga Yajin Cin Abinci

Rahotani daga Saudiyya na cewa Hamshakin mai kudin nan kuma dan gidan saurautar kasar Talal bn Abdul-Azez ya shiga yajin abinci.

Tashar Talabijin din Aljazira ta kasar Qatar ta habarta cewa hamshakin mai kudin ya shiga yajin cin abincin domin nuna rashin amincewarsa kan ci gaba da tsare  'ya'yansa uku a Otel din Ritz Carlton dake birnin Riyad.

Wasu majiyoyin kasar ta Saudiya sun ce tun a ranar 10 ga watan Nuwambar shekarar 2017 da ta gabata ce, dan gidan sarautar ta saudiya kuma hamshakin mai kudi na Duniya Talal bn Abdul-Azez mai shekaru 86 a Duniya ya fara yajin cin abinci bayan da ya samu labarin tsare 'ya'yan nasa.

Majiyar ta ce tun daga wannan lokaci aka umarci likitocin asibitin Malik bn Faisal da su rika ba shi abinci ta hanyar na'ura.

Tun a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ce, sarkin kasar Saudiya ya bada umarnin kafa kwamitin yaki da barnar dukiyar kasa bisa jagorancin dansa Muhammad bin salman, inda a cikin 'yan kwanaki kadan aka kame 'ya'yan gidan sarauta, wasu daga cikin ministoci da kuma wadanda suka gabata da dama.

To sai dai masu sharhi kan siyasar kasar ta Saudiya na ganin cewa  yawan kame-kamen da ake yiwa 'ya'yan gidan masarautar kasar, shiri ne na karfafa ikon Muhammad bn Salman dan sarkin na saudiya kuma mai jiran gado.

Tags

Jan 02, 2018 06:29 UTC
Ra'ayi