• Isra'ila Za Ta Bar Wani Bangaren Birnin Qudus Idan An Shiga Sulhuntawa Da Palasdinawa

Yawan yan majalisar dokokin HKI Knesset wadanda suka amince a bada wani bangare na birnin Qudus ga Palasdinawa a tattaunawan sulhu nan gaba ya karu daga 61 zuwa 80 daga cikin yan majalisa 120.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto kafafen yada labarai na HKI suna fadar haka a yau Talata . Labarin ya kara da cewa Palasdinawa suna bukatar gabacin birnin Qudus ne a matsayin cibiyar gwamnatinsu. 

Wannan shirin na saryar da wani bangare na birnin Qudus ga Palasdinawa  wanda majalisar ta Knesset ta ke yi ya samu karin amincewar majalisar ne bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da birnin Qudus a matsayin cibiyar gwamnatin HKI a cikin watan da ya gabata.

An dakatar da batun sulhuntawa tsakanin HKI da Palasdinawa ne tun shekara ta 2014.

 

Tags

Jan 02, 2018 11:47 UTC
Ra'ayi