• Yemen: An Hallaka  Sojojin Saudiyya 13 A Gundumar Asir

Tahsar talabijin din 'al-Masirah' ta kasar Yemen ta ce; an kashe sojojin Saudiyya ne a cikin gundumar Asir da ke kasar Saudiyyar

Sojojin kasar ta Yemen da kuma mayakan sa-sai na Ansarullah sun kai hari ne a cikin gundumar Asir da ke cikin Saudiyyar tare da kashe sojoji 13.

Harin na Sojoji da kuma dakarun sa-kai na kasar Yemen, ya zo ne a matsayin maida martani ga gare-haren da Saudiyyar take kai wa kasar ta Yemen na tsawon shekaru kusan uku a jere.

A jiya talata ma dai jiragen yakin Saudiyyar sun kashe fararen hula 10 a  gundumar Sa'adah.

Kawo ya zuwa yanzu dai Saudiyyar da abokan kawancenta sun kashe fiye da mutanen Yemen 13,000.

Tags

Jan 03, 2018 09:45 UTC
Ra'ayi