• Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada A Garin Ramallah Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan

Wani matashin bapalasdine ya yi shahada bayan fama da raunuka da ya yi sakamakon harin wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai yankin gabar yammacin Jordan na Palasdinu.

Majiyar asibitin Palasdinu ta sanar da cewa: Wani matashi mai suna Mus'ab Faras Attamimi dan shekaru 17 a duniya ya yi shahada a yau Laraba bayan jinya sakamakon harbinsa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a farmakin wuce gona da iri da suka kai kauyen Diru-Nizam da ke arewacin garin Ramallah a gabar yammacin kogin Jordan.

A dauki ba dadin da aka yi tsakanin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da suka kai farmaki kan kauyen Diru-Nizam da matasan Palasdinawa, sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wutan bindiga kan matasan lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatan Palasdinawa uku, inda daya ya yi shahada a yau Laraba 

Tags

Jan 03, 2018 19:26 UTC
Ra'ayi