• Sojojin Siriya Sun Kwato Filin Jirgin Saman Abul Zuhur Da Ke Idlib

Rahotanni daga kasar Siirya sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami nasarar kwato filin jirgin saman soji na Abul Zuhr da ke garin Idlib daga hannun kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra.

Kafar watsa labaran 'I'ilam al-Harb' da ke watsa labaran da suke da alaka da yaki da ta'addanci da ake yi a kasar Siriyan ya bayyana cewar a yammacin jiya Laraba ne sojojin Siriyan da suke samun goyon bayan dakarun kawayen Siriyan suka sami nasarar kwace filin jirgin saman sojin da ke kudu maso gabashin lardin Idlib daga hannun 'yan ta'addan Jabhatun Nusrah.

Kwace filin jirgin saman dai yana cikin irin ci gaba da nasarorin da sojojin Siriya da kawayenta suke samu ne a fadar da suke yi da kungiyoyin ta'addancin da suke samun goyon bayan kasashen waje a kasar ta Siriya.

A shekara ta 2015 ne dai 'yan ta'addan Jabhatun Nusra din suka kwace wanann filin jirgin sama na soji daga hannun dakarun Siriyan bayan kawanya na watanni da suka yi masa.

 

Tags

Jan 11, 2018 05:47 UTC
Ra'ayi