• An Sami Karuwar Masu Yawon Bude Ido A Kasar Syria A 2017

Ma'aikatar yawon bude-ido ta kasar Syria ta sanar da cewa fiye da mutane miliyan daya suka ziyarci kasar a 2017

A yau alhamis ne ma'aikatar yawon bude ido ta fitar da bayani da ya kunshi cewa idan aka kwatanta da shekarar 2016, an sami karuwar masu zuwa kasar da kaso 25%, inda a 2017 adadin mutanen da suka ziyarci Syria ya kai miliyan da 300,000.

Bayanin ya ce; A tsakanin maziyartan da akwai 161,000 da suka ziyarci wuraren addini ne.

Dawowar tsaro da zaman lafiya a mafi yawancin sassan kasar ta Syria da kuma murkushe kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh, sun karfafa masu yawon bude ido zuwa kasar.

Tags

Jan 11, 2018 11:14 UTC
Ra'ayi