• Majalisar Dinkin Duniya: Gina Sabbin Gidaje A Yankin Yamma Da Kogin Jordan Baya Bisa Ka'ida

Jami'a mai kula da harkokon Zaman Lafiya a gabas ta tsakiya na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa kudurin Haramtacciyar kasar Iraela na gina gidajen zama fiye da dubu a yankin yamma da kogin Jordan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Anotoly nakalto Nuckolay Mladenov yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma bukaci haramtacciyar kasar Israela ta dakatar da aikin.

A ranar Laraban da ta gabata ce gwanatin haramtacciyar kasar Israela ta bayyana amincewarta da shirin gina gidaje 1,100 a yankin yamma da kogin Jordan na kasar Palasdinu da ta mamaye.

Wata kungiya mai zaman kanta wacce take bincike kan lamuran Palasdinu ta bayyan cewa a cikin shekara ta 2017 da ta gabata kadai yahudawan Sahyoniyya sun kwace filaye masu fadin Hekta 900 daga hannun Palasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan don ginawa yan'uwansu gidajen zama. 

Tags

Jan 12, 2018 06:35 UTC
Ra'ayi