• Pira ministan Iraki: Za A Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa A Lokacin Da Aka Tsayar

Haydar Abadi ya ce a ranar 12 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2018 ne za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Haydar Abadi wanda ya gudanar da taron manema labaru a yau a birnin Bagadaza ya ci gaba da cewa; Ko kadan ba zai bude tattaunawa da wadanda suke son shigar da masu dauke da makamai a cikin fagen siyasa ba.

Har ila yau, pira ministan kasar ta Iraki, ya kira yi al'ummar kasar da su kaucewa sauraron jita-jita akan 'yan ta'adda da yiyuwar harin ta'addanci.

Akan yankin Kurdawa kuwa, Abadi ya ce yana matukar kokarin ganin an warware matsalar da yankin yake fama da ita.

 

Tags

Jan 16, 2018 18:46 UTC
Ra'ayi