Feb 08, 2018 06:50 UTC
  • Masar Ta Amince Wa Kasar Qatar Shigar Da Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza

A karon farko tun lokacin da da Masar ta katse dangantakar diblomasiyya da kasar Qatar, ta amince a shigar da tallafin kasar zuwa yankin Gaza.

Wata majiyar labarai ta Palasdinawa a yankin Gaza ta bada wannan labarin a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa kayayyakin agajin sun dade suna kan iyakokin kasashen biyu, ba tare da samun izinin shigar da su a yankin ba. 

Kamfanin dillancin Laraban IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Masar a karon farko ta bada izinin shigar da kayayyakin gine-gine wadanda suka hada da siminti sa sauransu zuwa cikin yankin na Gaza. 

Banda haka labarin ya ce za'a bude kofar kan iyakar yankunan biyu dake Rafah na kwanaku uku don bawa Palasdinawan yankin Gaza shiga kasar.

Gwamnatin kasar Masar dai tana bude kofar shiga yankin Gaza ta Rafah ne na kwanaki 17 a shekara, don abin da ta kira lalacewar harkokin tsaro a yankin Sinai.

Tun shekara ta 2006 ne Haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da killace yankin Gaza ta sama da kasa da kuma taruwa, tun lokacin yankin ba ya da mafita zuwa kasashen duniya.

Tags

Ra'ayi