Feb 08, 2018 06:51 UTC
  • Rikici Tsakanin Masar Da Turkiya Kan Ruwan Tekun Mediterranean

Dangantaka tsakanin kasashen Masar da Turkiya ta yi tsami a cikin yan kwanakin nan, saboda sanin iyakokin da kowanne daga cikin yake mallaka a tekun Mediterranean .

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ahmad Abu-Zaid kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar yarjejeniyar da kasar Masar ta cimma da kasar Cyprus kan iyakokin da kowanne daga cikinsu yake mallaka daga gabacin tekun Mediterranean ta zama doka ce, kuma duk wanda  yayi kokarin taka ta Masar zata kalubalance shi. 

Abu-Zaid ya kara da cewa yarjejeniyar rabon kan iyaka a cikin tekun Mediterranean , yarjejjeniya ce ta kasa da kasa wacce Majalisar dinkin duniya ta amince da ita. 

Amma ministan harkokin wajen kasar Turkiya Maulud Chavis-Uglu, a ranar litinin da ta gabata ce ya bada sanarwan cewa kasar Turkiya ba ta amince da yarjejeniyar da kasashen Masar ta Cyprus suka cimma kan rabon kan iyaka da kuma amfani da tekun Mediterranean a shekara ta 2013 ba. 

Tags

Ra'ayi