• Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Bayyana Razana Da  Makaman Hizbullah

Ministan Ilimi na Haramtacciyar Kasar ta Yahudawa Niftali Bint ne ya bayyana haka a yayin da ya ziyarci kan iyakar palasdinu da Lebanon

Niftali Bint ya ci gaba da cewa; Ana kara samun aman dar-dar akan iyaka da Lebanon, ga shi ba mu cikin shirin fuskantar Hizbullah.

Bugu da kari Bint ya yi ishara da harin da sojojin Sahayoniya suka kai a Syria, sannan ya kara da cewa; Ba za mu bari Iran ta kafa sansanin soja a cikin Syria ba.

A jiya laraba ne dai jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai harin ta'addanci da makamai masu linzami a kusa da birnin Damascuss.

Jiragen yakin sun harba makamai masu linzamin ne daga sararin samaniyar kasar Lebanon.

A nata gefen gwamnatin Lebanon ta bai wa sojojin kasar izinin mai da martani akan duk wani wuce gona da iri na 'yan sahayoniya.

Tags

Feb 08, 2018 12:21 UTC
Ra'ayi