Feb 09, 2018 11:54 UTC
  • Micheal Aun: Lebanon Za Ta Yi Turjiya A Gaban Wuce Gonar 'Yan Sahayoniya

Shugaban kasar Lebanon Micheal Aun ya furta haka ne a yayin da ya gana da mataimakin ministan harkokin Wajen Amurka David Satterfield da yake ziyara a Lebanon.

Shugaban na kasar Lebanon da ya gana da Satterfield a jiya Alhamis da dare, ya tattauna batutuwa da suke da alaka da gabas ta tsakiya tare da bakon nashi.

A shekaran jiya Laraba ne dai majalisar koli ta tsaron kasar Lebanon bisa jagorancin shugaba Micheal Aun, ta gabatar da taro, inda ta fitar da bayanin nuna kin amincewa da katangar da 'yan sahayoniya suke ginawa akan iyaka da Lebanon. 

Majalisar koli ta tsaron kasar Lebanon ta kuma bai wa sojojin kasar umarnin kalubalantar wuce gona da irin 'yan sahayoniya.

Amurka ta nuna damuwarta akan yiyuwar barkewar yaki a tsakanin Lebanon da haramtacciyar Kasar Isra'ila.

Tags

Ra'ayi