Feb 13, 2018 06:38 UTC
  • Ministan Ilimi A Isra'ila Ya Yi Kira Da A Kaucewa Aukuwar Yaki Tsakaninsu Da Lebanon

Ministan ma'aikatar ilimi a Haramtacciyar kasar Isra'ila ya kirayi gwamnatin yahudawan da ta yi taka tsantsan wajen kauce wa duk wani abin da ka iya jawo barkewar wani sabon yaki a tsakaninsu da Lebanon.

Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, ministan ilimin na haramtacciyar kasar Isra'ila Al Isra'ili Naftali Benet ya bayyana cewa, barkewar duk wani yaki a halin yanzu tsakaninsu da Lebanon, zai sanya Isra'ila ta fuskanci ruwan rokoki da makamai masu linzami, wanda ba taba ganin irinsa a tarihinta ba, yana mai ishara da irin martanin da Hizbullah za ta mayar a kansu.

Ya ce wajibi ne a kan gwamnatin Isra'ila ta dauki matakan kaucewa barkewar wani sabon yaki tsakaninta da Lebanon, domin hakan ba maslaha ce ga Isra'ila ba.

Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, tare da cikakken goyon baya daga Donald Trump na Amurka, yana kada kugen yaki a kan kasar Lebanon, da sunan yunkurin murkushe karfin kungiyar Hizbullah.

Tags

Ra'ayi