Feb 13, 2018 12:22 UTC
  • An Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 21 Kan Tsohon Ministan Kasuwancin Iraki

Majiyar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa kotun kasar ta yanke hukuncin daukrin shekaru 21 ga tsohon ministan kasuwancin kasar Afdulfatah Assudani

Majiyar ta ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan da ta kama shi da wasu laifuka guda uku da suka hada, da sakaci da aikinsa, gami da yin amfani da matsayinsa ta hanyar da ba ta dace ba.

A watan Satumbar 2017 ne jami'an  tsaron kasar Labnon suka cafke Sudani a birnin Beirut, sannan suka mika shi a hannun hukumomin kasar ta Iraki.

Wani jami'in tsaron Labnon ya bayyana cewa sun cafke Assudani ne bayan da suka samu umarnin hakan daga jami'an 'yan sanda na kasa da kasa.

Kafin wannan hukunci, a shekarar 2012, kotun kasar ta Iraki ta bayar wa tsohon Ministan kasuwancin na Iraki hukuncin daurin shekaru 7 a bayan idansa, bayan da ta same shi da laifin barnata dukiyar kasa.

Ra'ayi