Feb 14, 2018 06:18 UTC
  • FAO:Kashi 40% Na Albarkatun Gona Na Kasar Iraqi Sun Lalace Saboda Yaki Da Yan Ta'adda

Hukumar abinci da noma ta dunia FAO ta bada rahoton cewa kashi 40% na albarkatun noma na kasar Iraqi sun lalace sanadiyyar yaki da ta'addanci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya nakalto hukumar ta FAO tana fadar haka a jiya talata a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Ta kuma kara da cewa mutanen kasar Iraqi kimani miliyon 12 ne suke zama a karkara sannan sun dogara da noma don samun kudaden shiga. 

Labarin ya kara da cewa tun shekara ta 2014 a lokacin da mayakan Deash suke kwace yankuna da dama daga arewaci da kuma yammacin kasar ayyukan noma suka lalace a yankunan kuma mafi yawansu mutanen wadannan yankuna suka zama yan gudun hijira.

A shekara da ta gabata ce sojojin kasar Iraqi tare da mayakan sa kai na Hashdushaabi suka sami nasarar korar Daesh daga kasar. 

Tags

Ra'ayi