• Yarima Mai Jiran Gadon Masarautar Saudiyya Ya Yi Furucin Cin Mutunci Kan Al'ummar Qatar

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya ya yi furucin cin mutunci kan al'ummar Qatar ta hanyar bayyana cewar al'ummar Qatar ba su shige yawan mazauna hanya guda na kasar masar ba.

A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar: Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman ya bayyana cewa: Babu gaskiya a batun cewar kasashen da suka kakaba takunkumi kan kasar Qatar suna fuskantar matsin lamba kan su janyo daga kan matsayinsu.

Har ila yau Bin Salman ya yi furucin wulakanci kan al'ummar Qatar da cewa yawansu bai shige yawan jama'ar hanya guda ba a kasar Masar, kuma mahukuntan Qatar suna kiyayya da kasashen Saudiyya da Masar.

Tags

Mar 06, 2018 12:01 UTC
Ra'ayi