• Siriya : MDD, Ta Bukaci A Sake Bude Hanyoyin Shigar Da Kayan Agaji A Ghouta

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a sake bude hanyoyin shigar da kayan agaji a yankin gabashin Ghouta na kasar Siriya.

Wata sanarwa da babban sakatare na MDD, Antonio Guteres ya sanyawa hannu, ta bukaci dukkan bangarorin da batun ya shafa su taimaka wajen samar da hanyoyi mafo sauki don shigar da kai dauki wa al'ummar yankin.

Bayannai daga yankin na cewa har yanzu ana ci gaba da barin wuta duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Rasha ta ayyana a yankin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin tsaro na MDD zai yi taron gaggawa kan yadda har yanzu aiwatar da yarjejeniyar a yankin na ta cutura.

A ranar Litini data gabata, wani ayarin Komba na motocin agaji ya samu shiga Douma, saidai sa'o'i kadan bayan hakan ya fice sakamakon hare-hare.

 

Tags

Mar 07, 2018 05:47 UTC
Ra'ayi