• An Bankado Wani Yunkurin Harin Kunar Bakin Wake A Gundumar Salahaddin

An bankado wani shirin kai harin kunar bakin wake a garin Ishaqi a kudancin larsin Salahaddin na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria news ya bayar da rahoton cewa, wasu 'yan ta'addan takfiriyya sun yi nufin kaddamar da wasu munanan hare-hare a garin Ishaqi, amma jami'an tsaro sun rutsa da su, bayan samun wasu bayanan sirri kan shirin da 'yan ta'addan suke da shi.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hana 'yan ta'adda shiga cikin jama'a, inda daga karshe suka tarwatsa kansu da bama-baman da suke dauke da su, ba tare da wani farar hula ko jami'an tsaro ya rasa ransa ko samun rauni ba.

A cikin makon da ya gabata ma jami'an tsaron kasar ta Iraki sun gano wani shiri da kungiyar Daesh ta yi da nufin tarwatsa tashar wutar lantarki ta yankin na Salahddin, amma hakan bai nasara ba, bayan jami'an tsaron suka halaka dukkanin 'yan ta'addan da suke shirin kai hare-haren.

 

Mar 07, 2018 17:10 UTC
Ra'ayi