• Siriya : Amurka Ta Ce Za Ta Dauki Mataki, Idan Kwamitin Tsaro Ya Kasa

Amurka ta ce a shirye ta ke ta dauki mataki cikin har da kai hare hare a Siriya, muddun dai kwamitin tsaro na MDD ya kasa akan shirin tsagaita wuta a yankin gabashin Ghouta.

Wannan bayyani ya zo ne a yayin da Amurka ta shigar da wani sabon kudiri ga zaman MDD da ke neman tsagaita wuta na kwanaki 30 a yankin Gabashin Ghouta.

Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Nikky Haley ta shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar cewa tsagaita wutar da aka cimma aka amunce da shi a baya, bai yi  wani tasiri ba, kasancewar an gaya shigar da kayan agaji a yankin na Ghouta.

Kasashen yamma da Amurka dai na zargin Rasha da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar duk da cewa ta kada kuri’ar amincewa da hakan a gaban majalisar dinkin duniyar.

Jakadan Rasha a MDD, ya yi fatali da duk zarge zarge da ya danganta da marar tushe da ake ma kasarsa, wanda ya ce na cimma manufofin siyasar kasashen Turai da Amurka ne, ba tare da sun damu da ayyukan jin kai ba.

Tags

Mar 13, 2018 05:52 UTC
Ra'ayi