• Syria: An Gano Wani Wuri Da 'Yan Ta'adda Suke Kera Makamai Masu Guba A Ghouta

A jiya ne wasu daga cikin kafofin yada labarai da suke bin diddigin hakikanin abin da yake faruwa a Syria, suka bayar da rahotanni dangane da gano wani wuri da 'yan ta'adda takfiriyya suke kera makamai masu guba, a cikin yankin Aftaris da ke Ghouta a gabashin birnin Damascus, fadar mulkin kasar ta Syria.

A ci gaba da tsarkake yankin Ghouta daga 'yan ta'addan takfiriyya da sojojin kasar Syria ke yi, a ranar Lahadin da ta gabata sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan daga wasu yankuna na Ghouta, da suka hada har da Aftaris daya daga cikin yankunan da suke da matukar muhimmanci ga 'yan ta'addan.

'Yan jarida masu aika wa kafofin yada labarai daban-daban rahotanni da suke yin rakiya sojojin na Syria, sun bayar da rahotanni daga yankin na Aftaris cewa, a jiya Litinin, sojojin na Syria sun gano wani wuri da 'yan ta'adda suke harhada makamai masu dauke da sanadarin sarrin mai guba, daga ciki kuwa har da wadanda an gama hada su ana shirin harba su.

Tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne, jakadan kasar Syria a majalisar dinkin duniya Dr. Bashar Ja'afari, ya mika wa babban sakataren majalisar dinkin duniya wasu rahotanni da gwamnatin Syria ta samu ta hanyar bayanai na sirri, kan shirin da 'yan ta'addan suke da shi na harba makamai masu guba a cikin 'yan lokutannan a cikin yankin na Ghouta.

Ja'afari ya ce sun mika wadannan bayanai ne domin yanke hujja, domin kuwa tabbas 'yan ta'addan sun samu horo daga kasashen turai da ke mara musu baya da kuma Turkiya kan yadda ake harhada wadannan makamai da kuma yadda za a yi amfani da su, da kuma yadda za su tsara lamarin domin dora alhakin hakan a gwamnatin Syria, wanda duniya ta saba da jin irin wannan wasan kwaikwayo, wanda ake shiryawa domin cimma manufofin siyasa a kan gwamnatin kasar ta Syria.

Ya ce ko shakka babu, gagarumar nasarar da sojojin Syria suke samu a halin yanzu a kan 'yan ta'addan takfiriyya, ya dagula dukkanin lissafin da kasashen da suke daukar nauyinsu na turai da kuma na larabawa suke da shi a kan gwamnatin Syria, a kan haka a halin yanzu Amurka da kawayenta suna neman su samar da wani dalili komai karancinsa domin tuhumar Syria da kuma matsa lamba  a kanta, domin 'yan ta'adda su samu su lumfasa, ko kuma su samu hanyar tsrewa daga wurare da aka rutsa da su, wanda hakan ne ya sanya jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya ta yi barazanar cewa za su kai ma gwamnatin Syria hari idan majalisar dinkin duniya ta kasa tabbatar da tsagaita a yankin Ghouta.

Babban abin tambaya a na shi ne, mene ne yasa kasashen turai da kafofin yada labaransu ba su da wata magana a kan Syria sai dai batun Ghouta? alhali akwai wasu yankuna da ake rikici a kasar tsakanin sojoji da 'yan ta'adda, kuma  a kullum suna magana a kan cewa sojojin Syria na kai hare-hare a kan fararen hula, ba tare da yi wa duniya cikakken bayani ba  a kan hakikanin abin da yake faruwa a Ghouta, kan cewa 'yan ta'adda ne daga kasashen duniya suka kafa babbar tunga da muggan makamai a yankin na Ghouta da ke kusa da birnin Damascus, suna harba makaman roka a kan birnin a kullum rana suna kashe mutane, wanda a ko a jiya Litinin sun harba makaman roka kan Damscus sun kashe mutane 6 da jikkata wasu, ba tare da wata kasar turai ko wata kafar yada labaran turai ta nakalto wannan labarin ba. Shin ko akwai wata kasa daga cikin kasashen turai ko na larabawa da za ta amince da hakan? ta yaya dubban 'yan ta'adda daga kasashen duniya suka shiga Syria har suka kafa sansani da tarin muggan makamai a Ghouta? shin gwamnatin Syria ba ta hakkin ta kare kasarta da al'ummarta? amsar da ya kamata kasashen turai da kafofin yada labaransu su baiwa duniya kenan.

Ko shakka babu gano wadannan sanadarai masu guba maboyar 'yan ta'adda a yankin Ghouta, ya kara tabbatar da irin mummunan shirin da kasashe masu daukar nauyion 'yan ta'adda suke da shi a kan gwamnatin Syria musamman Amurka, Birtaniya da Faransa da kuma Isra'ila, wanda ya yi kama da abin da suka aikata a kasar Libya, inda suka kifar da gwamnati suka rusa kasar, suka mayar da ita a halin da take ciki a yanzu.To amma ko gwamnatin ta Syria a shirye take ta mika wuya ga matsin lambar turawa da farfagangar da suke yi  a kanta dare da rana? Bayanin da rundunar sojin kasar ta Syria ta fitar a jiya, ya tabbatar da cewa a halin yanzu ta tsarkake fiye da rabin yankin Ghouta daga 'yan ta'addan takfiriyya duk da wannan farfaganda da karairayi na gwamnatocin kasashen turai da 'yan korensu da kuma kafofin yada labaransu, kuma ana ci gaba da bude hanyoyi domin kubutar da fararen hula da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su tare da hana su fita daga yankin, wanda kuma hakan shi ne babban dalilin da ya sanya sojojin Syria suke yin taka tsantsan matuka wajen kai hare-hare a kan 'yan ta'addan, domin suna fakewa ne a  cikin wurare na fararen hula a mafi yawan lokuta.

Wannan bayani na rundunar sojin ya kara tabbatar da cewa, ba a shirye suke su mika wuya ga matsin lambar 'yan mulkin mallaka ba, kuma a shirye suke su kare kasarsu

Mar 13, 2018 16:16 UTC
Ra'ayi