• Sojojin Yamen Sun Kashe Sojojin Saudiyya Masu Yawa A Kudancin Kasar Ta Saudiyya

Sojojin Yamen sun bude wuta kan gungun sojojin marautar Saudiyya a yankunan Jizan da Asir da suke kudancin kasar ta Saudiyya, inda suka kashe sojoji akalla bakwai.

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar da suke tsaron kan iyakar kasarsu sun yi kwanton bauna wa ayarin sojojin Saudiyya a yankunan garuruwan Jizan da Asir a jiya Talata, inda suka kashe sojojin Saudiyya akalla bakwai tare da jikkata wasu adadi masu yawa.

Har ila yau sojojin Yamen sun kashe sojojin Saudiyya uku a kauyen garin Jizan a ranar Litinin da ta gabata. Kamar yadda sojojin Yamen suka yi luguden wuta kan gungun sojojin Saudiyya a yankin arewacin lardin Hujjah da ke shiyar arewa maso yammacin kasar Yamen. 

Tags

Mar 14, 2018 06:27 UTC
Ra'ayi