• Kasashen Iran, Iraki, Siriya Da Rasha Sun Sha Alwashin Kawo Karshen Ta'addanci A Yanki G/Tsakiya

Kasashen Iran, Iraki, Siriya Da Rasha sun bayyana wajibcin karfafa cibiyar hadin gwiwa a tsakaninsu da ke birnin Bagadaza da nufin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radiyo da Talabijin na Iran, cikin wani rahoto da ya watsa, ya jiyo ministan tsaron kasar Iraki Arfan al-Hayali, a wata ziyara da ya kai cibiyar hadin gwiwa tsakanin kasashe hudun da ke birnin Bagadaza yana fadin cewa nasarorin da aka samu wajen raunana kungiyoyin ta'addanci a kasar Iraki sun samo asali ne sakamakon hadin gwiwan gwamnatocin kasashen Iran, Siriya da Rasha da kuma gwamantin Irakin.

Shi ma a nasa bangaren wakilin Iran a wannan cibiyar Birgediya Janar Mustafa Muradiyan ya bayyana wajibcin ci gaba da kiyaye irin wannan hadin gwiwa da ake da shi tsakanin wadannan kasashen yana mai sake jaddada aniyar Iran ta ci gaba da wannan aiki na ganin bayan kungiyoyin ta'addanci a yankin Gabas  ta tsakiya.

Ita dai wannan cibiyar an kafa ne da nufin hadin gwiwa tsakanin wadannan kasashe hudu da nufin kawo karshen kungiyoyin 'yan  ta'addan da suke samun goyon bayan wasu kasashen duniya da suke yaki a Iraki da Siriyan.

Tags

Mar 14, 2018 11:07 UTC
Ra'ayi