• Qassemi Ya Bayyna Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya A Matsayin Maras Masaniya

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qassemi ya bayyana Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bn Salman a matsayin wani mutum maras masaniya wanda bai san inda duniya ta dosa ba, wanda babu bukatar a bata lokaci wajen mayar masa da martani.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a daren jiya a yayin da yake mayar da martani ga kalaman batancin da Yariman na Saudiyya yayi kan Iran inda ya ce Iran dai kasa ce da take girmama kowace kasa ba tare da la'akari da girma, karfin soji ko tattalin arziki ko kuma tasirin da take da shi ba, kamar yadda kuma take fatan ganin an sami tsaro da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.

Mr. Qassemi ya kara da cewa kalaman Yariman na Saudiyya suna tunatar da irin yanayin zamanin jahiliyya lokacin da hankali ba shi ne a gaba yana mai cewa kamata yayi kasar da shekaru uku kenan ta gagara tabuka komai a gaban al'ummar Yemen marasa kariya ta san matsayinta kana kuma ta yi shiru a gaban kasa ma'abociya karfi da daukaka irin Iran.

A jiya ne dai Yarima mai jiran gadon na Saudiyya a wata hira da yayi da tashar talabijin din CBS ta Amurka ya bayyana Iran a matsayin kasa mai hatsari ga zaman lafiyan Gabas ta tsakiya yana mai barazanar cewa matukar Iran ta kera makamin nukiliya  to Saudiyya ma cikin karamin lokaci za ta kera, lamarin da ya zamanto abin wargi da zolaya ga Yariman a kafafen watsa labarai.

Tags

Mar 16, 2018 11:10 UTC
Ra'ayi