Mar 16, 2018 19:26 UTC
  • Dan Gwagwarmayar Palasdinawa Ya Halaka Sojojin H.K.Isra'ila biyu Tare Da Jikkata Wasu Na Daban

Wani dan gwagwarmayar Palasdinawa ya halaka sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila biyu tare da jikkata wasu hudu na daban a gabar yammacin kogin Jordan.

Tashar talabijin ta 14 mallakin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta watsa rahoton cewa: Wani dan gwagwarmayar Palasdinawa ya kaddamar da harin kwantan bauna kan wata motar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a mashigar matsugunin yahudawa 'yan kaka gida na Maftu-Doutan da ke kudancin garin Janin a gabar yammacin kogin Jordan, inda ya kashe sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila biyu tare da jikkata wasu hudu na daban.

Rahoton ya kara da cewa: Biyu daga cikin sojojin da suka jikkata suna cikin mummunan hali, kuma maharin ya samu nasarar tserewa bayan kai harin.

 

Tags

Ra'ayi