• Rundunar Sojin Siriya Ta Sanar Da 'Yantar Da Kashi 70% Na Yankin Ghouda

Rundunar sojin Siriya ta sanar da 'yantar da kashi 70 cikin dari na yankunan Ghouda ta Gabas da suke karkashin mamayar gungun 'yan ta'adda.

A bayanin da rundunar sojin Siriya ta fitar a yau Juma'a ta bayyana cewa: Sojojin gwamnatin Siriya sun samu nasarar yantar da yankunan Ghouda ta gabas da ke gefen birnin Damasqas fadar mulkin kasar daga mamayar gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasar ta Siriya.

Bayanin ya kara da cewa: Sojojin Siriya sun fafata da gungun 'yan ta'adda a yankuna da dama na Ghouda ta Gabas, inda suka murkushe 'yan ta'addan tare da 'yantar da garuruwa da kauyuka gami da gonaki da kuma lambuna daga mamayar 'yan ta'addan.

A halin yanzu haka dubban al'ummar Ghouda ta Gabas sun samu nasarar ficewa daga yankunan da a baya suke karkashin killacewar gungun 'yan ta'adda. Kamar yadda sauran yankunan na Ghouda kimanin kashi 30 cikin dari suke karkashin ikon 'yan ta'adda sakamakon garkuwa da suka yi da fararen hula tare da amfani da su a matsayin kariya daga hare-haren sojojin na Siriya.

Tags

Mar 16, 2018 19:27 UTC
Ra'ayi